Menu

Su Waye Ke Juya Akalar Hakar Ma’adanai A Niger, Yayin Da Mutane 37 Suka Mutu Hannun Jami’an Tsaro?

By Editor 23 hours ago 9
Spread the love

An cafke Matas 37 Yayin wani samamen jami’an Tsaro a Wushishi/Lukoto bisa zargin su da Hakar Ma’adanai ba bisa ka’ida ba, Daga bisani aka ce sun mutu a hannun hukumar Tsaron al’umma ta civil Defence.

Bayan faruwar abin, Gwamnatin jiha ta Bada Umarnin bin bahasi, Yan sanda Zasu gudanar da bincike, Sauran Hukumomin Tsaro suma sun kaddamar da bincike. An dakatar da kwamandan Civil Defence na jihar, wannan kawai Wasu matakai ne, ba a Kai ga gano gaskiyar al’amarin ba

Ba a tuhumi Wadannan matasa da Ayyukan Ta’addaci ba, abin da ya bayyana shi ne suna kokarin Neman na Kan su ne Domin iyalan su, su Kuma tallafawa iyayen su, amma Gwamnatin jihar ta gaza samar musu da ingantaccen Tsarin sana’ar.

Tambayar da ke fitowa Daga bakin duk wani Mai hankali ita ce, waye ya Bada Umarnin kama su ? Har zuwa lokacin da sakamakon bincike zai bayyana, za a Ci Gaba da danganta lamarin da yuwuwar barkewar wata cuta, ko guba ko cinkoso ko suma, dole ne a yi bincike ba wai Daukar matakai Kan zato ba.

Hatta Wurin Hakar Ma’adanan ba zai ware shi Wajen bincike ba. Akwai zarge-zargen cewar Wasu Masu Fada aji a jihar, sun dauki lokaci suna son kwace wannan Wurin Hakar Ma’adanai, akwai bukatar bincika wannan Ikirarin.

Ana Yan gulmace-gulmace da tsaigungumi a garin Minna, cewar kamar abinda ake zargin ya faru a Zamfara, Gwamnan jihar Niger nada sha’awar mallakar Wurin, Kuma akwai ana cewar akwai shiri na sauyawa al’ummar Wushishi gari da sunan tsaftace muhalli.

Har ila yau, an rawaito cewar ya je wuraren Hakar Ma’adanan da yawa, Kuma ma ana zargin cewar ana bashi wani kaso duk mako Daga zinare, abinda aka ce ya Sanya shi dukan kirji da alfahari a wani lokaci a Baya, Wadannan manyan dalilai ne. Ba wai sheda bace, Wadannan batutuwan sune a takaice ake tattaunawa .

Wadannan batutuwan sun Isa a bukaci amsar su, waye yake Neman a bashi izinin Hakar Ma’adanai? Waye ya tura bukatar lasisi ko Kuma a Sayar Masa da Wurin Hakar Ma’adanan? Shin akwai Wadanda Suka yi yunkurin karbe iko da Wurin a Baya? Ko akwai wata bukatar Dake Kasa Kafin cafke Wadannan matasa? Shin ko akwai shi ne shiri na tsaftace muhalli a Wushishi da batun sauya mutanen sa gari Kafin samamen jami’an Tsaro?
A barin kundin bayanai su fayyace, ya kamata a gayyaci Hukumar da’ar ma’aikata da kotun ta su kallo batun bayyana Kadarorin da kundin lasisi da bayanan kwamitin karta kwana da Kuma bayanan kasuwar hada-hadar gwala- gwalai.

Rade-radin da ake a Minna shi ne Hakar Ma’adanai a jihar Niger ba fagen marasa galihu ba ne. Bada lasisi hakkin Gwamnatin Tarayya ne, tafiyar da wuraren hakar Kuma na hannu gwamnatocin jihohi. Daraktan lura da albarkatun Kasa Ademola Banjo Gwamnan ne ya nada shi a shekara ta 2024, bincike ya nuna cewar ma’aikacin banki ne kuma Dan kasuwa. Baya Cikin aikin sa Bada hayar wuraren hakar Ma’adanai Babu batun rajistar Masu harkar, ga Kuma kwamitin karta kwana Kan Hakar Ma’adanai ta haramtaciyyar hanya.akwai tambayoyi da yawa irin Wadannan.


Babu Wanda zai baka wannan bayani, ko akwai Wanda zai Fada Maka Wanda ya San adadin gwal din Dake fita Daga Niger ta hannun dilallai Masu lasisi da Kuma Sauran hanyoyi.

Babu Wanda zai fake karkashin Rashin Tsarin hukuma a fannin Hakar Ma’adanai ya kaucewa doka, duk abinda aka Tabbatar kamata ya yi a Kai kotu, Bai kamata su mutu ba saboda a kulle su, Kuma Neman abinci Cikin Ramin Ma’adanai ba shelar Yaki bane.

Ya kamata a fitar da sahihin Tsarin bincike a bainar jama’a, a fadi jami’in da ya Bada Umarnin Kamo Matasan da sashin da ya aikwatar da yanayjn da aka saka su da Kuma bayanin waye ya amfana ko zai amfana idan aka share Wurin.

Jihar Niger ta cancanci Wadannan bayanai da iyalai 37 Dana ‘yan Najeriya Gaba daya

Daga Ibrahim Maigida Shehu, Maitumbi, Minna.

Leave a Reply

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *