Menu

NCC Ta Ƙaddamar da Sabuwar Manhaja don Yaƙi da Satar Wayoyi da Jabun Na’urori

By Editor 13 hours ago 2
Spread the love

Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC) ta bayyana cewa sabuwar manhajar tantance sahihancin wayoyin salula, wato Device Checker Platform, za ta taimaka wajen rage satar wayoyi da kuma dakile yaɗuwar jabun na’urorin sadarwa a ƙasar.

Hukumar ta ce an ƙirƙiri manhajar ne domin ƙarfafa bin ƙa’idojin amincewa da na’urorin sadarwa da aka fi sani da Type Approval, da kare masu amfani da wayoyi, tare da tabbatar da ingancin na’urorin da ake amfani da su a hanyoyin sadarwar wayar hannu a Nijeriya.

Babbar Manajar Fasaha da Ingancin Hanyoyin Sadarwa ta NCC, Miss Kingi Bayi, ce ta bayyana hakan a wani taron manema labarai kan ƙa’idojin fasaha da ingancin hanyoyin sadarwa na shiyyoyin hukumar, wanda aka gudanar a ofishin shiyyar NCC da ke Kano ranar Alhamis.

A cewarta, an tsara manhajar ne domin tabbatar da cewa na’urorin sadarwa da ake amfani da su sun cika ƙa’idojin inganci da ake buƙata kafin su yi aiki a kan hanyoyin sadarwar wayar hannu.

Ta ƙara da cewa amfani da wannan fasaha zai taimaka wajen rage matsalar satar wayoyin salula da kuma hana yaɗuwar wayoyin jabu a kasuwannin Nijeriya.

Tun da farko, shugaban ofishin shiyyar NCC na Kano, Injiniya Maigana Gidado, ya bayyana cewa ƙaddamar da shirin wani mataki ne na ƙarfafa bin ƙa’idojin hukumar, kare masu amfani da na’urorin sadarwa da kuma dakile shigowa da sayar da na’urorin bogi ko waɗanda aka yi wa kwafi ba tare da izini ba.

Ya ce shirin na daga cikin ƙoƙarin hukumar na tabbatar da cewa na’urorin sadarwa da ake amfani da su a Nijeriya sun cika ƙa’idojin amincewa da inganci da aka shimfiɗa.

A cewar Injiniya Gidado, manufar taron manema labaran ita ce sanar da al’umma halin da ake ciki game da aiwatar da tsarin tantance na’urorin sadarwa na NCC, wanda aka tsara domin ƙarfafa bin ƙa’idojin amincewa da na’urori, kare masu amfani da su da kuma inganta ingancin na’urorin da ke aiki a hanyoyin sadarwar ƙasar.

Ya kuma bayyana cewa hukumar ta samu ci gaba wajen aiwatar da shirin, musamman ta hanyar tsara tsarin rajista da bayar da lasisi ga dillalan wayoyi, tare da wayar da kan masu shigo da na’urorin sadarwa da sauran masu ruwa da tsaki a masana’antar.

Bugu da ƙari, ya ce NCC ta sauƙaƙa hanyoyin neman lasisi da daidaita harkokin dillalan na’urorin sadarwa da ƙa’idojin da ake buƙata. Wannan mataki, a cewarsa, ya taimaka wajen bai wa dillalai da dama a Jihar Kano damar samun lasisin gudanar da harkokinsu.

Hukumar ta bayyana cewa waɗannan matakai na daga cikin ƙoƙarinta na inganta sahihancin na’urorin sadarwa, kare haƙƙin masu amfani da su da kuma tabbatar da bin ƙa’idoji a masana’antar sadarwa ta Nijeriya.

Leave a Reply

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *